Isa ga babban shafi
Kaduna

Najeria-fursunoni a Kaduna sunyi bore

Fursunoni biyu ne suka rasa rayukansu a Kaduna yayinda wasu 41 suka sami munanan raunuka sakamakon wani kazamin bore da fursunonin suka yi yau a gidan yarin Kaduna. Harkoki da dama agarin Kaduna sun kusa tsayawa saboda fargaban abinda wannan bore ka iya haifarwa. 

Le vice-président nigérian Goodluck Johnatan.
Le vice-président nigérian Goodluck Johnatan. AFP/Wole Emmanuel
Talla

Jamiin gidan yarin Olusola Ogundipe ya shaidawa wakilinmu cewa fursunoni 39 da maaikatan gidan yari biyu ne suka sami raunukan.

Ya fadi cewa fursunonin na bore ne domin cunkoso da dadewa gidan sarka ba tareda yanke masu hukunci ba.

A cewar Jamiin gidan yarin an tsara domin fursunoni 524 to amma ayanzu haka akwai fursunoni 790.

Hukumomin kulada yancin dan adam sun sha nuna munin gidajen sarka dake kasar amma kuma Hukumomin kasar basu dauki lamarin da wani muhimmanci ba.

Shugaban kasar Umaru Musa Yaraduwa  ayanzu haka samada watanni 5 basuyi ido hudu ba, da Mataimakinsa Goodluck Jonathan, wanda shine yake rike da mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.