Isa ga babban shafi

Adadin yaran da ke mutuwa a kasa da shekaru biyar ya ragu a duniya-MDD

Majalisar dinkin duniya ta ce adadin yara kanana da ke mutuwa a shekaru biyar zuwa kasa ya ragu matuka a 2022, idan aka kwatanta da baya.

Yara 'yan kasa da shekaru 5 na cikin hadarin mutuwa a saboda raunin garkuwar jikin su.
Yara 'yan kasa da shekaru 5 na cikin hadarin mutuwa a saboda raunin garkuwar jikin su. ©UNICEF/YPN-Alaa Noman
Talla

Ta cikin wani rahoto da ta fitar, majalisar ta ce shekarar 2022 itace wadda aka fi samun karancin yaran da suka mutu.

Yara kasa da miliyan 5 ne suka mutu a shekarar ta 2022, adadin da ake ganin yayi kasa kwarai da abinda aka saba gani.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, daraktan lafiya na asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya Helga Fogstad ya ce an sami wannan nasara ne sakamakon tallafi bayan da kasashe ke samu kan yaki da cututtukan da ke saurin hallaka kananan yara.

Kasashen Malawi, Rwanda da Mongolia sune suka fi samun ci gaba a fannin tabbatar da mutuwar kananan yara, kuma hakan ta samu ne da goyon bayan bankin duniya.

Majalisar dinkin duniya ta kuma ce an samu cigaba a fannin horas da ungozoma da sauran jami’an jinya, da kuma karbar rigakafin da ta dace kan cututtukan da ke yiwa kananan yara barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.