Isa ga babban shafi

Biyu cikin bakwaini 39 da ake cikin fargabarsu a wani asibitin Gaza sun mutu

Wasu jarirai biyu bakwaini sun mutu sakamakon katsewar wutar lantarki a babban asibitin Gaza, kamar yadda kungiyar likitoci ta Isra’ila ta sanar a wannan Asabar, yayin ake gwabza fada a kusa da rukunin Asibitin Al-Shifa.

Ana fargabar bakwaini 39 za su mutu a Gaza bayan katsewar lantarki a asibiti
Ana fargabar bakwaini 39 za su mutu a Gaza bayan katsewar lantarki a asibiti DR
Talla

Kungiyar likitocin Isra'ila ta da sanar da matakin, tace wasu bakwaini 37 na cikin hadarin mutuwa saboda sashin da ake kula da su a asibi ya daine aiki saboda katsewar hutan lantarki.

“Sakamakon rashin wutar lantarki, za mu iya cewa sashin kula da jirarai bakwaini ya daina aiki, wanda ya yi sanadin mutuwar jarirai biyu, kuma akwai hadari ga rayukan wasu jarirai 37” a asibitin Al-Shifa”.

Sama da makwanni biyar tun bayan barkewar yakin da ya kai ga katse wutan lantarki, asibitoci da sauran cibiyoyin kula da lafiya sun dogara ne da injina ko janareta, amma kuma duk tsawon wannan lokaci babu wani mai ko da lita daya da ya shiga yankin zirin Gaza, lamarin da ya kai ga asibitoci fuskantar cikas wajen samar da lantarki.

An yi wa asibitoci kawanya

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun ce an killace asibitin ta yadda baza a iya shigar da mara lafiya ko wadanda suka jikkata ba.

Sai dai rundunar sojin Isra'ila ta musanta batun killace asibitin, inda dubban mazauna yankin suka fake, yayin da sojoji ke fafatawa da mayakan Falasdinawa a yankin.

Devant l'hôpital al-Shifa, à Gaza, le 10 novembre 2023.
Harabar asibitin Al-Shifa da ke yankin Gaza. 10/11/23 © Khader Al Zanoun / AFP

An ji karar harbe-harbe da fashewar abubuwa a harabar Asibitin Al-Shifa na Gaza a wannan Asabar, kuma na’urar daukar hoton kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya tabbatar da lamarin.

Kisan kare dangi

Kungiyoyin suka ce hotunan abin da ke faruwa a harabar asibitin, ya fi karfin ace wani bala’in jinkai, sai dai a kira shi da hukuncin kisa ne na gama-gari.

Tun farko ministan lafiya na Falasinawa ya ce jarirai bakwaini guda 39 wadanda ke cikin kwalba na cikin hatsarin mutuwa a asibitin Al-Shifa da ke Gaza.

Likitocin Falasdinawa na kula da jaririn bakwaini a asibitin Al Aqsa da ke Deir el-Balah, a zirin Gaza, Lahadi, 22 ga Oktoba, 2023. (AP Photo/Adel Hana)
Likitocin Falasdinawa na kula da jaririn bakwaini a asibitin Al Aqsa da ke Deir el-Balah, a zirin Gaza, Lahadi, 22 ga Oktoba, 2023. (AP Photo/Adel Hana) AP - Adel Hana

Duk da cewa jariran na cikin kwalba, to amma katsewar wutar lantarki na nufin cewa iskar da suke amfani da ita ma za ta katse.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.