Isa ga babban shafi

Macron ya goyi bayan likitoci su taimakawa wadanda suka gaji da duniya su mutu

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana goyon bayan sa ga sabon kudurin dokar da ta baiwa mutane a kasar damar neman taimakon likitoci wajen mutuwa, yayin da ya ce nan ba da jimawa gwamnati zata mikawa majalisa wannan doka don amincewa da ita.

UKRAINE-CRISIS/CZECH-FRANCE
UKRAINE-CRISIS/CZECH-FRANCE REUTERS - David W Cerny
Talla

Kasashe makwaftan Faransa wato Switzerland, Belgium da Netherlands sun jima da fara amfani da wannan doka da take baiwa mutane damar neman tallafin likitoci wajen mutuwa.

Wannan doka dai zata baiwa marasa lafiya ko kuma wadanda suka gaji da duniya damar neman tallafin likitoci su kashe su ta hanyar amfani da kimiyya ba tare da wata illa ga lafiya ba.

Macron ya jima yana nuna alamun amincewa da wannan doka, sai dai yana dar-dar sakamakon yadda manyan malaman kirista mabiya darikar katolika a kasar ke chachakar ta.

Tun 2016 ne ake ta cece-kuce game da doka, yayin da ake ta musayar yawu da karon hujjoji a tsakanin masu goyon baya da kuma sukar ta.

A wata tattaunawa da Jaridar Liberation ta kasar, Macron ya ce zai kyautu a sauyawa dokar suna daga taimakon kashe kai, zuwa samun taimakon likitoci don mutuwa cikin sauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.