Isa ga babban shafi
Faransa - Coronavirus

Faransa zata karrama ma'aikatan lafiya da suka yaki annobar korona

Gwamnatin Faransa na shirin karrama jami’an kiwon lafiya da suka taka muhimiyar rawa a lokacin da cutar Covid 19 ta  bullu a kasar. Sanarwar da mai magana da yahun gwamnatin kasar Sibeth Ndiaye ta fitar ta samu karbuwa daga 'yan siyasar kasar.

Ma'aikaciyar lafiya dake kula da masu dauke da cutar korona  2021.
Ma'aikaciyar lafiya dake kula da masu dauke da cutar korona 2021. AP - Andre Penner
Talla

A makon da ya gabata ne mai magana da yahun gwamnatin Faransa Sibeth Ndiaye ta sanar da shirin gwamnati na karrama jami’an kiwon lafiya da suka sadaukar da rayuwar su a kokarin ceto rayukan marasa lafiya bayan bulluwar cutar covid 19 a Faransa.

Ta na mai magana yayin wani taron manema labarai 'yan lokuta da kamala taron majalisar Ministocin kasar a karkashin jagrancin shugabancin Emmanuel Macron.

Tun a tsakiyar watan Afrilu ne wasu daga cikin 'yan majalisun dokokin kasar da suka hada da Catherine Dumasv da Damien Adam suka shigar da bukatar ganin an yi amfani da bukukuwan zagayowar ranar jamhuriya na 14 ga watan Yuli na shekarar bana don karama jami’an kiwon lafiya da suka taka muhimiyar rawa tun  lokacin da kwayar cutar Covid -19 ke kisa cikin al’uma.

Wadanan 'yan majalisu sun aike da wasika  ga Shugaban kasar ta Faransa, inda suka bukaci hukumomin kasar da kada su manta da 'yan kasuwa da direbobin sufuri, malaman makarantu da leburori da ilahirin su sun taka muhimiyar rawa a lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.