Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Matasa za su fara karbar rigakafin Covid-19 a Faransa

Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da shirin fara yiwa ilahirin Faransawan da shekarunsu ya kai 18 zuwa 50 rigakafin Covid-19 nan da watan Yuni mai zuwa, matakin da ke zuwa a dai dai lokacin da kasar ke shirin sassauta dokar kulle.

Fiye da mutum miliyan 15 suka karbi alluran rigakafin covid-19 rukunin farko a Faransa.
Fiye da mutum miliyan 15 suka karbi alluran rigakafin covid-19 rukunin farko a Faransa. REUTERS - BENOIT TESSIER
Talla

Emmanuel Macron wanda ke sanar da matakin ta shafinsa na Twitter ya ce daga ranar 15 ga watan Yuni za a bude rijistar allurar ga matasa ‘yan shekaru 18 zuwa 50 yayinda wadanda shekarunsu ya haura 55 kuma su ke cikin wani yanayi ka iya rijistar don karbar allurar.

Matakan na Faransa ya biyo bayan yunkurin Macron na bude kasar da kuma sassauta dokar takaita walwalar da kasar ke fuskanta bayan tsanantar cutar a zagaye na 3.

Gabanin kalaman na Macron, ministan lafiya na Faransar Olivier Veran ya sanar da shirin bude wani sabon gangamin rigakafin a ranakun karshen mako da zai shafi mutum miliyan 4 ciki har da matasan da shekarunsu ya fara daga 18 zuwa 50 amma masu fama da wata cuta da ke musu barazanar kamuwa da Covid-19.

Ministan lafiyan na Faransa ya bayyana cewa,  matasa masu cutukan da ke da alaka da zuciya ko hawan jini ko kuma kibar da ta wuce kima su ne sahun gaba da za su karbi rigakafin a wannan karon.

Cikin fiye da mutum miliyan 15 da suka karbi rigakafin na Covid-19 zagayen farko a Faransa, kashi 29 na adadin ne kadai matasa la’akari da yadda aka karkata alluran don cetar rayukan dattijai da tsaffi wadanda suka fi barazanar kamuwa da cutar.

Haka zalika mutum miliyan 5 da dubu 600 da suka karbi dukkan alluran biyu kashi 12 na alkaluman ne kawai matasa, wanda ke nuna gibin da kasar ke da shi wajen yi wa matasa rigakafin duk da ya ke ta fara shawo kan yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.