Isa ga babban shafi
MDD

MDD ta dauki mataki akan IS

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya jefa kuri’ar amincewa da wani daftari domin kange hanyoyin da kungiyar mayakan IS da ke da’awar jihadi a Syria da Iraqi ke samun kudaden shiga. Bayanai sun kungiyar da ke ci gaba da gudanar da ayyukanta a kasashen Iraqi da Syria, na samun milyoyin daloli ta hanyar cinikin man fetur da kuma karbar kudaden fansa sakamokon yin garkuwa da mutane.

Taron Manyan kasashe 20 na duniya suna tattauna matakan yakar Mayakan IS na Iraqi
Taron Manyan kasashe 20 na duniya suna tattauna matakan yakar Mayakan IS na Iraqi REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Masana dai na ganin wannan matakin zai yi tasiri wajen dakile ayyukan ISIL.

Farfesa Umar Pate na Jami’ar Bayero a Kano Najeriya ya ce idan aka samu nasarar dakile hanyoyin samun kudaden Mayaka IS dan lokaci kadan ne abubuwa za su rincabe ma su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.