Isa ga babban shafi

Kasashen duniya na ci gaba daura damarar yaki da mayakan ISIS

Manyan kwamandojin kasashen da ke fada mayakan jihadi a kasar Syria da kuma Iraqi na shirin gudanar da taro yau talata a birnin Washington na kasar Amurka, domin kara daura damarar yakar magoya bayan wannan kungiya da ke ci gaba gwabza fada da kurdawa a zagayen birinin Kobani na Syria. Akwai manyan kwamandojin soja daga kasashe akalla 22, da za su halarci wannan taro na birnin Washington, kuma daga bisani za su gana da shugaban Amurka Barack Obama. A wani bangare kuwa, hukumomin kasar Turkiyya sun musanta sanarwar da hukomomin Amurka suka bayar, da ke cewa kasar ta amince Amurka ta yi amfani da sansanoni da kuma sararin samaniyar Turkiyyar domin kai wa mayakan jihadin hare-hare a Syria.Wasu dai na ganin bayanan na Turkiyya a matsayin nuna damuwa dangane da yadda Amurka ta fallasa wannan yarjejeniya, yayin da wasu ke ganin cewa ba wani abu mai kama da haka da kasashen suka cimma matsaya a kai. 

Wani dan kabilar Yazidi mai neman ganin an kawar da 'yan kungiyar ISIS
Wani dan kabilar Yazidi mai neman ganin an kawar da 'yan kungiyar ISIS REUTERS/Wolfgang Rattay
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.