Isa ga babban shafi
Iraq-MDD

Iraqi ta kai hari a yankunan dake hannun 'yan kungiyar ISIS a arewacin kasar

Dakarun kasar Iraqi sun fasa wata mafakar Mayakan Jihadi da ke a Garin Amerli na ‘ya Shi’a, inda dubban mutane suke makale fiye da Watanni 2 da suka gabata, cikin wani hali na rashin isasshen rbinci da ruwan sha mai tsabta.Kama wurin na matsayin babbar nasara ga dakarun na Iraqi, tun bayan da ‘yan tawayen kungiyar ISIS suka mamaye yankin.Kai farmakin ya biyo bayan wani kwarya-kwaryan harin da Amurka ta kai a yankin, inda ta yi ta ruwan wuta ta sama, kan ‘yan tawayen kungiyar ta ISIS.Sojan saman Amurka sun yi aikin ne tare da jiragen saman kasashen Australiya, Fransa da Ingila.Haka kuma an bada labarin cewar jiragen yaki daga kasashe daban daban ne suka yi ta jibge kayan agaji a yankin Amerli, na ‘yan kabilar Turmen na lardin Salaheddin.A baya dai Jakadan Majalisar Dinkin Duniya Nickolay Mladenov ya yi kashedin cewar suna sane da kisan gillar da ‘yantawayen ke yi a yankin.Amma ya ce Dakarunsu sun samu kutsawa a Amerli kuma wannan babbar nasara ce.Kasar Amurka da kanta ta bada labarin cewar ta kaddamar da kai farmaki sau 3 ta sama a yankin, kuma hakan ya nuna cewar a karon farko Amurkar na fadada yankunan da take kai hare-hare a kasar ta Iraqi zuwa Arewaci.Kasar Amurkar dai ta ce tana kaddamar da kai hare-haren ne da manufar dakushe kungiyar ISIS amma ta nisanta kanta daga duk wata alaka da kasar Siriya wadda ita ma ke fada da ‘ya’yan kungiyar ta ISIS. 

Wasu mayaka 'yan jihadi a kasar Iraqi
Wasu mayaka 'yan jihadi a kasar Iraqi REUTERS/Youssef Boudlal
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.