Isa ga babban shafi
Iraq

Harin da aka kai a masalllacin kasar Iraqi ya tunzura 'yan Sunni

Jami’an gwamnatin kasar Iraqi suna can suna kokarin kewantar da hankulan ‘yan kasar, bayan wani harin da ‘yan bindiga suka kai wani masallacin mabiya sunni, yayi sanadiyyar mutuwar mutane 70. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu hare haren da aka kai birnin Bagadaza da gewaye suka yi sanadiyyar mutuwar wasu mutanen 30.Harin masallacin na lardin Diyala, da wasu shaidun gani da ido suka ce mayakan ‘yan shi’a ne suka kai, na barazanar sake fusata mabiya Sunni marasa rinjaye a kasar.Gwamnatin kasar ta Iraqi, karkashin ‘yan Shi’a na ci gaba da neman goyon bayan ‘Yan Sunni, don kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasar. 

Prime Ministan Iraqi, Nouri al-Maliki.
Prime Ministan Iraqi, Nouri al-Maliki. IRAQ-SECURITY/ALISULEIMAN REUTERS/Thaier Al-Sudani/Files
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.