Isa ga babban shafi
Iraq-MDD

MDD ta bukaci ‘Yan siyasar Iraqi su kai zuciya nesa

Majalisar Dinikin Duniya ta gargadi jami’an tsaron kasar Iraqi su kaucewa tsoma baki a rikicin siyasar, da ya taso sakamakon nada sabon Firaminista da aka yi a kasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar barkewar wani sabon rikici a kasar.

Haider Abadi, sabon Firaministan Iraqi
Haider Abadi, sabon Firaministan Iraqi Reuters/路透社
Talla

Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi wannan kiran ne a daidai lokacin da hukumomin kasar Amurka da Iran, suka yi amanna da nadin Haidar al-Abadi, a matsayin sabon Firaministan kasar tare da kiran a kafa gwamnatin da za ta kunshi dukkan ‘yan kasar.

Abadi ne zai maye gurbin Nuri al-Maliki, da aka sauke daga mukamin shi, bayan ‘yan tawayen kasar sun yi ta kai hare haren da suka karbe yankunan da ke kan iyakar kasar da Syria.

Ban Ki Moon yace nasarorin da mayakan na Jamhuriyar musulunci suka samu a kasar, bai rasa nasaba da rashi shigar da dukkan masu ruwa da tsaki ciki gwamnatin al Maliki ta mabiya shi’a.

Majalisar ta Dinkin duniya ta nemi gwamnatocin kasashen Duniya su kai dauki ga dubun dubatar ‘yan Yazidi, marasa rinjaye, da suka tsere wa rikicin da ake yi zuwa tsaunin Sinjar a arewacin kasar ta Iraqi, sakamakon barazana daga ‘yan tawayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.