Isa ga babban shafi
Iraq-Syria

Kasashen Larababa suna neman mafita kan yakin Iraqi da Syria

Minitocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun gudanar da wani taro na musamman, domin tattauna batun yaduwar tashin hankalin kasashen Siriya da Iraqi, da kuma Karin yawan kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a yankin.Taron ya zo ne a dai dai lokacin da kasar Amurka, da ta kaddamar da kai farmakin sama a yankin arewacin kasar Iraqi, ke ci gaba da duba yiyuwar daukar irin wannan matakin, ga mayakan jihadi na IS a kasar ta Siriya.Ministocin harkokin wajen kasashen na Larabawa da suka halarci taron sun hada da Masar, Saudi Arebiya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar da Jordan.Ministocin sun gudanar da taron birnin Jidda kasar Saudi Arebiya cikin sirri.Ministocin, sun kuma tattauna batun tashin hankalin kasar Siriya, da yanda yake dada fadada, kazalika da kalubalen da suke fuskanta kan yawaitar masu tsattsauran ra’ayi a kasashen Larabawa.Ministocin sun bayyana cewar sun tattauna yadda za su iya shiga domin magance masalar, da ke kokarin game yankin na kasashen Larabawa.A cikin makon daya gabata, mayakan na kasar Iraqi suka fidda wani hoton bidiyo, da ke nuna yadda suka fille kan wani Dan Jaridan Amurka mai suna James Foley, lamarin da ya sa hukumomin birnin washigton suka yiwa shugabannin kasashen Larabawan kashedi.  

Ministan harkokin wajen Saudi Arebiya, Saud bin Faisal bin Abdelaziz
Ministan harkokin wajen Saudi Arebiya, Saud bin Faisal bin Abdelaziz AFP PHOTO / FAYEZ NURELDINE
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.