Isa ga babban shafi
Amurka-Iraqi

Hukumar FBI ta tantance mayakan IS da suka kashe 'yan jarida

Hukumar ‘yan sanda da ke fada da masu aikata manyan laifufuka a kasar Amurka FBI, ta ce ta tantance wadanda suka kashe ‘yan jaridar kasar James Foley da kuma Steven Sotloff a lokacin da ake garkuwa da su ko dai a Syria ko kuma a Iraki.

Shugaban FBI James Comey daga hagu.
Shugaban FBI James Comey daga hagu. REUTERS/Gary Cameron
Talla

Shugaban hukumar ta FBI James Comey da kansa ne ya tabbatar da hakan a birnin Washington, to sai dai bai yi karin bayani a game da asalin kasashen da maharan suka fito ba.

Har ila yau Comey ya ce yanzu haka suna ci gaba da binciken wani faifan bidiyo da ke nuna wani na turanci kamar Ba’amurke inda yake yin kira da a shiga jihadi domin fada da manufofin kasashen Yamma.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.