Isa ga babban shafi
Iraq-Syria

Mayakan Daular Islama sun kori mutanen Syria

Kungiyar da ke sa ido a rikicin Syria tace Mayakan da suka ayyana kafa sabuwar daular Islama sun kori mutane kimanin 30,000 daga gidajensu a garin Shuheil da ke gabacin Syria. Kungiyar tace Mayakan sun kori mutanen ne bayan sun karbe ikon garin daga hannun mayakan Al Nusra.

Mayaka masu gwagwarmayar kafa daular Islama a Iraqi
Mayaka masu gwagwarmayar kafa daular Islama a Iraqi AFP PHOTO/HAIDAR HAMDANI
Talla

Haka kuma akwai wasu kimanin 30,000 da aka tursasawa kauracewa gidajensu a biranen Khosam da Tabia Jazeera da kuma gabacin yankin Deir Ezzor.

Mayakan na ISIS Sun mamaye wani yanki ne na Syria da Iraqi tare a ayyana kafa sabuwar daular Islama.

Yanzu haka kuma Jami’an tsaron Iraqi suna kokarin tantance sakon bidiyo da aka nuna shugaban Mayakan Abu Bakr Baghdadi a karon farko yana gabatar da hudubar Juma’a a birnin Mosul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.