Isa ga babban shafi
Mexico

Jami’an tsaron Mexico sun cafke shugaban masu fataucin miyagun kwayoyi na kungiyar Zetas

Hukumomi a kasar Mexico sun bayyana yin wani babban kamu, wanda ya basu damar cafke shugaban kungiyar dake safarar muggan kwayoyi a kasar. Wannan kamu a cewar rahotanni na daya daga cikin babbar nasara da jami’an tsaron kasar ta Mexico suka samu a ci gaba da yaki da ake yi da safarar muggan kwayoyi a kasar, inda suka cafke shugaban kungiyar da ake kira Zetas wato Miguel Angelo Trevino.  

Jami'an tsaro cafke da wasu masu safarar kwayoyi a kasar Mexico
Jami'an tsaro cafke da wasu masu safarar kwayoyi a kasar Mexico Reuters
Talla

Trevino wanda aka fi sani da inkiyar Z-40 ya kasance shugaba a harka safarar kwayoyi da aikata manyan laifuka da aka fi tsoro a kasar ta Mexico wanda bai mayar da ran dan adam komai ba, kamar yadda rahotanni ke cewa.

Cafke Trevino ya zo ne watanni takwas bayan dakarun kasar sun kashe wanda ya gada a kungiyar ta Zetas wato Heriberto Lazcano a wani artabu da suka yi, wanda daga baya wasu mutane dauke da makamai suka sace gawarsa a lokacin da ake shirin yi masa jana’iza.

An dai haifi Trevino ne a yankin Nuevo Laredo dake kasar ta Mexico amma ya fi gudanar da harkokinsa ne a Birnin Dallas dake Jihar Texas a kasar Amurka.

A yanzu haka kuma yana tsare ne a yankin na Nuevo Laredo dake Arawa maso gabashin Jihar Tamaulipas dake kan iyaka da kasar Amurka.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.