Isa ga babban shafi
Mexico

An cafke wata babbar Jami’ar Gwamnatin kasar Mexico

Hukumomin Kasar Mexico sun gurfanar da shugabar kungiyar malaman kasar, Elba Esther Gordillo a gaban kotu, inda suke zargin ta da yin rubda ciki da kudaden al’umma.An kama Gordillo ne ranar Talata, inda ake tuhumarta da almundahana na Dala miliyan 200, wanda ake zargin ta yi amfani da su wajen sayayya a Amurka da kwaskwarimar fuskarta da sayan kadarori da kuma jirgin sama.

Esther Gordillo 'Yar kasar Mexico
Esther Gordillo 'Yar kasar Mexico Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.