Isa ga babban shafi
Mexico

An cafke jagoran masu fataucin miyagun kwayoyi na kasar Mexico

Jami’an tsaro a kasar Mexico, sun ce sun yi nasarar kama Miguel Angel Trevino, da ake kira Z-40, shugaban kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta kasar.

Miguel Trevino da aka fi sani da suna Z-40.
Miguel Trevino da aka fi sani da suna Z-40. Reuters
Talla

Jami’an sun ce sun kama Trevino ne lokacin da ya sauka daga jirginsa mai saukar ungulu, zai shiga motarsa akan iyakar Texas, inda suka same shi da tsabar kudi Dala miliyan 2, da makamai, da kuma ‘yan rakiya.

Kakakin ma’aikatar cikin gidan kasar, Eduardo Sanchez, ya ce ko harsashi guda ba’a harba ba lokacin kamen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.