Isa ga babban shafi

Koriya ta Kudu za ta gudanar da atisayen soji mafi girma a tarihi

Koriya ta kudu zata fara wani sintirin sojoji mafi girma kuma irin sa na farko cikin shekaru 10, don nunawa duniya irin karfin soja da kuma tarin makaman da ta ke da su a birnin Seol.

Shugaba Yool ya ce lokaci yayi da kasar zata nunawa duniya cewa a shirye take ta fuskanci kowacce irin barazana
Shugaba Yool ya ce lokaci yayi da kasar zata nunawa duniya cewa a shirye take ta fuskanci kowacce irin barazana REUTERS - JONATHAN ERNST
Talla

Yayin sintirin sojojin, wanda za a gudanar da misalin karfe 4 na yammacin yau, wanda ya yi dai-dai da ranar tunawa da ‘yan mazan jiya ta kasar, inda dakaru za su jeru tsahon kilomita 2 a tsakiyar babban birnin kasar Seol.

Bayanai sun ce akalla sojoji dubu 7 ne zasu bada gudunmuwa a wannan atisaye, yayin da kasar za ta yi bajekolin nau’ukan makaman yaki fiye da 340, da suka hadar da bindigogi, alburusai, tankokin yaki, makaman artillary da jiragen yaki marasa matuka da sauransu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban kasar Yoon Suk-yeol, ya bayyana aniyar daukar tsatsauran mataki kan makwafciyarta Koriya ta Kudu, wadda ke yawan nuna mata yatsa, da kuma yi mata barazana da makamai.

Da ya ke bayani a sansanin sojojin sama na Seongnam, shugaba Yool ya gargadi Koriya ta Arewa game da yunkurin mayar da mummunan mataki kan wannan atisaye da za ta yi, inda ya ce  matukar ta yi wannan gigin tabbas zai kawo karshen makaman nukiliyar da ta ke ikirarin mallaka ba bisa ka’ida ba.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da rashin jituwa da yunkurin afkawa juna da yaki ke ci gaba da kamari a duniya, yayin da kasashe ke rige-rigen mallakar manyan makamai da kuma nuna su ga duniya da nufin yiwa kasashen da ke kawo musu wargi barzana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.