Isa ga babban shafi
Amurka-Koriya ta Arewa

Koriya ta Kudu za ta yi gwajin makamin nukiliya - Amurka

Amurka ta ce ta yi amannar cewa Koriya ta Arewa tana shirin  gwajin makamin nukilya a cikin wannan watan na Mayu da muke ciki, karo na farko tun bayan shekarar 2017, tana mai sabanta tayin tattaunawa don warware tankiyar da ke tsakaninsu

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fito da wannan sanarwar ne a daidai lokacin da hankalinta ke ci gaba da tashi a game da Koriya ta Arewar, wadda ta gudanar da gwajin makamai har 14 tun daga watan Janairu zuwa yanzu.

Nan gaba a cikin wannan watan, shugaban Amurka Joe Biden zai yi tattaki zuwa Japan da Koriya ta Kudu, inda ake sa ran batun Koriya ta Arewa zai kasance a sahun gaba a cikin abubuwan da za su tattauna.

Gwajin da Koriya ta Arewar za ta yi na iya zuwa daidai lokacin ziyarar shugaba Biden, ko kuma ranar 10 ga watan Mayu, lokacin rantsar da zababben shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol, wanda ya sha alwashin daukar tsatsaurar matsaya a kan Koriya ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.