Isa ga babban shafi

Koriya ta Arewa ta kaddamar da sabon jirgin ruwan kai hari da makamin nukiliya

Koriya ta Arewa ta sanar da kaddamar da wani jirgin ruwan karkashin teku da ta kwashe shekaru da dama tana kerawa, matakin da shugaba Kim Jong Un ya bayyana a matsayin mai matukar muhimmanci a kokarinsa na samar da jiragen ruwan yaki masu amfani da makamin nukiliya domin tunkarar Amurka da kawayenta na Asiya.

A cikin wannan hoton da gwamnatin Koriya ta Arewa ta fitar, ya nuna sojojin ruwan kasar da shugaba Kim Jong Un, da wasu mukarrabansa gaban wani sabon jirgin ruwa na nukiliya da kasar ta kera mai "Hero Kim Kun Ok" bukin kaddamarwa da ya gudan ranar Laraba, 6 ga watan Satumbar shekarar 2023.
A cikin wannan hoton da gwamnatin Koriya ta Arewa ta fitar, ya nuna sojojin ruwan kasar da shugaba Kim Jong Un, da wasu mukarrabansa gaban wani sabon jirgin ruwa na nukiliya da kasar ta kera mai "Hero Kim Kun Ok" bukin kaddamarwa da ya gudan ranar Laraba, 6 ga watan Satumbar shekarar 2023. AP
Talla

Kamfanin Dillancin Labaran Koriya ta Arewa ya ce jirgin mai suna "Hero Kim Kun Ok" an kera shi ne don harba makaman kare-dangi daga karkashin ruwa, sai dai bai bayyana adadin makaman da zai iya dauka ko harbawa ba.

A cikin wannan hoton da gwamnatin Koriya ta Arewa ta fitar, ya nuna shugaban kasar Kim Jong Un, da wasu jami’an tsaro gaban wani sabon jirgin ruwa na nukiliya da kasar ta kera mai "Hero Kim Kun Ok" bukin kaddamarwa da ya gudan ranar Laraba, 6 ga watan Satumbar shekarar 2023.
A cikin wannan hoton da gwamnatin Koriya ta Arewa ta fitar, ya nuna shugaban kasar Kim Jong Un, da wasu jami’an tsaro gaban wani sabon jirgin ruwa na nukiliya da kasar ta kera mai "Hero Kim Kun Ok" bukin kaddamarwa da ya gudan ranar Laraba, 6 ga watan Satumbar shekarar 2023. AP

A cikin jawabansa a wurin taron kaddamar da jirgin a ranar Laraba da kuma lokacin da ya shiga cikin jirgin a ranar Alhamis, Kim ya bayyana jin dadinsa da cewa kasar ta samu nata jirgin ruwan na nukiliya domin tinkarar sojojin ruwan Amurka.

Amurka

A watan Yulin ya da gaba, Amurka ta girka wani jirgin ruwa na makamin nukiliya a gabar ruwan Koriya ta Kudu a karon farko tun shekarun 1980.

Shugaba Kim ya ce, kasar tana kera wani sabon jirgin ruwa mai sarrafa makamashin nukiliya tare da shirin sake fasalin jiragen karkashin teku da saman ruwa ta yadda za su iya sarrafa makaman kare dangi, yana mai bayyana inganta tsaron kasar ta fannin ta karfin nukiliya a matsayin wani matakin gaggawa.

A cikin wannan hoton da gwamnatin Koriya ta Arewa ta fitar, ya nuna wani sabon jirgin ruwa na nukiliya da kasar ta kera mai "Hero Kim Kun Ok" bukin kaddamarwa da ya gudan ranar Laraba, 6 ga watan Satumbar shekarar 2023.
A cikin wannan hoton da gwamnatin Koriya ta Arewa ta fitar, ya nuna wani sabon jirgin ruwa na nukiliya da kasar ta kera mai "Hero Kim Kun Ok" bukin kaddamarwa da ya gudan ranar Laraba, 6 ga watan Satumbar shekarar 2023. AP

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.