Kasashen Larabawa sun kaddamar da harin sama a Yemen
Kasashe biyar ne suka karba wa kiran da hukumomin kasar Yemen suka yi na a taimaka ma ta domin yaki da mayakan Huthi wadanda kawo yanzu suka mamaye muhimman yankuna na kasar.
Wallafawa ranar:
Kasashen Saudiyya, Bahrain, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuweit, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Abdur Rabo Mansur Hadi, yayin da kungiyar kasashen Larabawa ta bukaci a yi amfani da karfin soja domin fatattakar mayakan na Huthi.
Kasashen Saudiyya, Maroko, Pakistan, Jordan da Sudan, sun amince da kai hare haren soja musamman ta sama domin kare kasar, yayin da Iran da kuma Iraki suka nuna rashin amincewarsu da haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu