Yemen
Mansur Hadi Ya sake neman bukatar haddin kai MDD akan rikicin kasar Yemen
Shugaban Kasar Yemen Abdurrabu Mansur Hadi ya sake bukatar kwamitin sulhu na majalisar Dinkin Duniya da ya amince da wani sabon kudiri da zai hana fadada hare haren mayakan Houthi dake neman kama garin Aden inda ya samu mafaka
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
A wasikar da ya aikewa Jakadan Faransa dake shugabancin kwamitin, Hadi ya bayyana fargabar cewar kungiyar Al Qaeda na iya anfani da halin da ake ciki wajen lalata al’amura a cikin kasar.
Ya kuma bukaci majalisar da ta karbe makamai masu linzamin da yanzu haka yan tawayen suka kwace daga rumbun ajiyar gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu