Shugaba Hadi ya tsere daga birnin Aden
Rahotannin daga kasar yemen na cewa Shugaba Abedrabbo Mansur Hadi ya gudu daga birnin Aden inda yake mafaka, a kokarin sa na tserewa mayakan Huthi, da a yanzu haka ke dab da isa fadar gwamnatin Aden
Wallafawa ranar:
Fada na ci gaba da tsananta a kasar ta yemen, inda a yanzu yan tawayen huthi sun karbe ikon sansani soji dake kusa da fadar gwamntin Mansur Hadi a kudanci Aden, kwanaki kalilan bayan kasar Amurka ta janye dakarun ta daga yankin
Wasu rahotanin sunce Shugaba Hadi yayi amfani da jirgi mai sauka angula ta fadar Al-Maasheeq wajen ficewa daga birnin Aden
Yanzu dai sansani sojin Al-Anad na karkashin iko mayakan Huthi bayan wata musayar wuta da taimakon yan tawayen kasar masu goyon bayan tsohon shugaba Abdallah Saleh da kuma dakarun gwamnati Hadi
Tuni dai kasar saudiya ta aike da dakarunta iyakar kasar ta da Yemen domin kare kasar ta daga barazanar tsaro
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu