Isa ga babban shafi
Birtaniya-Syria

Fiye da mutane dubu 200 sun mutu cikin shekaru 4 a rikicin kasar Syria

A karshen makon da ya gabata ne aka cika shekara 4 da fara yakin kasar Syria a kokarin kifar da gwamnatin shugaba Bashar al Assad, abinda yayi sanadiyar kashe mutane sama da 215,000 inji wata kungiyar dake sa ido kan yakin, da ke da cibiya a kasar Birtaniya.Kungiyar tace ya zuwa yanzu ta kididdige mutanen da aka kashe sun kai 215, 518 daga watan Maris na shekarar 2011 zuwa ranar 15 ga watannan na Maris, kuma 66,000 daga cikin mamatan fararen hula ne.Kungiyar tace a cikin makwanni uku da suak wuce kawai an kasha mutane 5,000 abinda ke nuna munin yakin na kasar Syria.Kungiyar ta kuma ce cikin fararen hular da aka kashe 10,808 yara kanana ne, kana kuma 7,000 daga cikin su mata ne.Daga bangaren gwamnati, kungiyar tace sojoji 46,138 suka mutu, tare da masu goyon bayan su 30,000.Kungiyar ta kuma ce sojojin haya daga kasashen waje 3.401 aka kasha, cikin su harda yan kungiyar Hezbollah, bayan wasu mutane 20,000 da suka bata wadanda ba’a san inda suke ba. 

Yakin Syria yayi sanadiyyar rasa ran mutane 215,000 cikin shekaru 4
Yakin Syria yayi sanadiyyar rasa ran mutane 215,000 cikin shekaru 4
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.