Isa ga babban shafi
Korea ta Kudu

Korea ta kudu ta yi tayin tattaunawa da Arewa

Shugabar kasar Koriya ta kudu Park Geun-Hye ta nemi hukumomin koriya ta arewa su amince kasashen biyu su hau teburin sasantawa, don kawo karshen kallon kaji da suke wa juna. Shugabar da ke jawabi yau juma’a a lokacin bukin tunawa da kawo karshen mamayar da Japan ta yi wa Koriya, ta bayyana takaicin da gwajin makamai masu linzami da hukumomin birnin Pyongyang suka yi a kwanakin nan.

Shugabar Koriya ta Kudu Park Geun-hye
Shugabar Koriya ta Kudu Park Geun-hye REUTERS/Yves Herman
Talla

Dama koriya ta arewa tace gwajin makaman na a matsayin martani kan atisayen soja na hadin gwiwa da Amurka ke yi da Koriya ta Kudu a kan iyakarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.