Isa ga babban shafi
Korea ta Kudu

Korea ta Kudu zata wargaza Jami'an tsaro a Teku

Shugabar Kasar Koriya ta kudu, Park Geun-hye ta ce zata wargaza jami'an tsaron tekun kasar saboda sakacin da aka same su da yi wajen aikin ceton dalibai sama da 300 da suka mutu a wani hadarin jirgin ruwa a kasar. Shugabar ta kuma nemi gafarar al'ummar kasar, inda tace za'a kafa wata sabuwar runduna da zata dace da zamani, bayan ta dauki alhakin matsalar da aka samu a matsayinta na shugaba.

Shugabar Korea ta Kudu Park Geun-hye a gaban faranni tana gaisuwar juyayin wadanda suka mutu a hadarin jirgin ruwa a teku.
Shugabar Korea ta Kudu Park Geun-hye a gaban faranni tana gaisuwar juyayin wadanda suka mutu a hadarin jirgin ruwa a teku. Reuters
Talla

A ranar 16 ga watan Afrilu ne jirgin ruwa ya kife a teku inda aka samu mutuwar mutanen Korea ta kudu kimanin 300 galibinsu Yara kanana daliban Makaranta.

Jirgin ruwa yana dauke ne da mutane 325, kuma an tabbatar da mutuwar 286, yayin da 18 suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.