Isa ga babban shafi
Korea-China

China da Korea ta Kudu za su hade wa Korea ta arewa kai

Kasashen China da Korea ta Kudu sun bayyana aniyarsu ta ganin an kwancewa Korea ta Arewa damarta ta Nukiliya. Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin guiwa da shugabannin kasashen biyu suka fitar a lokacin da suke ganawa a birnin Seoul.

Shugaban China  Xi Jinping tare da Shugabar korea ta Kudu Park Geun-hye suna ganawa a Seoul
Shugaban China Xi Jinping tare da Shugabar korea ta Kudu Park Geun-hye suna ganawa a Seoul Reuters
Talla

Sanarwar hadin guiwa da suka fitar shugaban China Xi Jinping da na Korea ta Kudu Park Gean-Hye sun kara nanata adawar da suke da Makaman Nukiliya a yankin ta Korea, amma kuma ana ganin kamar kansu a rabe ne akan batun tinkarar kasar Korea ta Arewa da yadda za’a gamsar da ita ta ajiye ko lalata Makaman Nukiliyarta.

Sai dai shugaba Park ta shaidawa manema labarai cewar bangarorin biyu duka sun amince su yi amfani da kowace irin hikima domin tabbatar da batun hana amfani da Makamin nukiliya a yankin na korea.

Wannan kuwa a cewar Shugabar hakan na iya yiyuwa ta hanyar tattaunawa a tsakanin kasashen da kuma kasar Korea ta Arewa da ake ganin ta yi nisa, bata jin kira a kan shirinta na tanadin Makaman Nukiliya.

A shekarun baya dai kasar Korea ta Arewa ta yi gwajin Makaminta na Nukiliya da akasarin kasashen yammacin Duniya kamar Amurka mai shiri da korea ta kudu ke kallon hakan a matsayin barazanar tsaron Duniya baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.