Isa ga babban shafi
Japan

Japan zata dage wa Korea ta Arewa Takunkumi

Firaministan kasar Japan Shinzo Abe yace zai janye wasu takunkumi da kasar ta kakabawa Korea ta Arewa bayan bangarorin biyu sun tattauna da juna game da batun sace wasu ‘Yan kasar Japan.

Firaministan kasar Japan  Shinzo Abe
Firaministan kasar Japan Shinzo Abe Reuters
Talla

Shinzo Abe ya fada wa manema labarai cewa Korea ta Arewa ta nuna alamar son a sasantaw bayan wakilan bangarorin biyu sun gana a Beijing akan batun sanin makomar was daruruwan ‘Yan kasar Japan da Korea ta Arewa ta kwace tsakanin 1970 zuwa 1980.

Firaminsitan yace akwai fahimtar juna da suka samu a zaman tattaunawar da aka gudanar a tsakaninsu da Korea ta Arewa.

Amma sai a gobe Juma’a ne Japan zata Janye Takunkumin idan Korea ta Arewa ta kafa kwamitin bincike a Pyongyang.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.