Isa ga babban shafi
Syria

An rantsar da Assad na Syria a wa'adi na uku

Shugaban kasar Syria Bashar Assad ya yi rantsuwar zarcewa da mulkin kasar wa'adi na uku yau, tare da yin gargadi da kakkausar murya ga kasashen dake taimakawa ‘yan tawaye a kasar sa.Rantsuwar da ya yi da alkurani mai girma, gaban  wakilan majalisar kasar,  a wani  zaman ta na  musamman , na zuwa ne watanni 40 da fara yaki cikin kasar da yayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu 160.

Wasu magoya bayan Shugaba Assad a Syria
Wasu magoya bayan Shugaba Assad a Syria REUTERS/Khaled al-Hariri
Talla

Shugaban kasar Syria Bashar Assad wanda yake hannun ka mai sanda ga kasashen yammacin turai, Amurka da kasashen larabawa dake goyon bayan masu fafutukan kawar da shi, yace zasu biya farashin taimakawa ta’adanci da suke yi.

A jawabin nasa bayan yayi rantsuwa na kama sabon wa'adi na tsawon shekaru bakwai, cewa abubuwan da ake gani yau a Iraq da Lebanon , da sauran kasashen da ake samun rikici, ya isa ishara gameda abinda yake cewa, kuma za a ga sakamakon nan bada dadewa ba.

Assad ya bayyana shi ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 3 ga watan yuni, a yankunan kasar kashi 88% dake hannun sa, inda aka bayyana ya zubar da wasu ‘yan takara biyu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.