Isa ga babban shafi
Syria-Jordan

An kashe wani Kwamandan ‘Yan tawayen Syria

‘Yan sandan kasar Jordan sun tabbatar da mutuwar wani kwamandan rundunar Mayakan Liwa al-Mujahideen da ke yaki a Syria tare da cewa ‘Yan uwansa ne suka kashe shi a Amman babban birnin kasar Jordan.

Mayakan Kungiyar Liwa al-Mujahideen da ke yaki a Syria
Mayakan Kungiyar Liwa al-Mujahideen da ke yaki a Syria REUTERS/Molhem Barakat
Talla

Jami’an tsaro sun ce an harbi Maher Rahhal ne har sau biyu da harsashen bindiga a ranar Juma’a wanda ke jagorantar Mayakan Liwa al-Mujahideen daya daga cikin kungiyoyin da ke gwagwarmayar kifar da gwamnatin Bashar al Assad na Syria.

‘Yan sandan Jordan sun ce ‘Yan uwansa ne suka kashe shi sakamakon wani rikici da ke tsakaninsu, kodayake ‘Yan sandan sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike.

Shugabannin gamayyar kungiyoyin ‘Yan tawayen Syria sun yi Allah waddai da kisan a wani sako da suka wallafa a shafinsu na Intanet tare da zargin gwamnatin Assad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.