‘Yan adawa a Syria sun tube kwamandansu
Gwamnatin ‘Yan adawa a Syria ta tube kwamandan mayakan da ke yaki da dakarun Bashar al Assad akan zargin yin rub da ciki da kudadensu. Wannan na zuwa ne a yayin da Amurka ke shirin ware kudi dala Miliyan 500 domin bayar da horo ga ‘Yan tawayen.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sanarwar da ‘Yan tawayen suka fitar a Facebook, Shugabansu Ahmad Tohme yace sun kaddamar da bincike akan Kwamandan dakarun ‘Yan tawayen Janar Abdelilah al Bashir.
Sanarwar kuma na zuwa a dai dai lokacin da Shugaban Amurka Barack Obama ya nemi Majalisa ta amince da kudi dala Miliyan 500 domin bayar da horo tare dab a ‘Yan tawayen na Syria makamai.
Akwai tattaunawa da Sakateren Harakokin Wajen Amurka John Kerry zai gudanar tare da ‘Yan tawayen Syria da mahukuntan Saudi Arebiya a birnin Jeddah.
An shafe tsawon shekaru uku ‘Yan tawaye suna yakin kawo karshen mulkin Bashar Al Assad a Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu