Isa ga babban shafi
Syria

za a yi zaben shugaban kasar Syria a ranar 3 ga watan Yuni

A ranar 3 ga watan Yunin wannan shekara ne za’a gudanar da zaben shugabancin kasar Syria, kamar yadda shugaban Majalisar dokokin kasar Mohamed al Laham ya sanar

Shugaban Syria Bashar Assad
Shugaban Syria Bashar Assad REUTERS
Talla

A wannan talata ne aka bukaci masu bukatar tsayawa takara a wannan zabe da su soma gabatar da takardunsa a gaban hukumar zabe, kuma suna da damar ci gaba da ajiye takarar tasu har zuwa ranar 1 ga watan Mayun gobe.

Ta la’akari da yanayin da kasar ke ciki na yakin basasa, wannan ya sa tuni manazarta suka yi hasashen cewa gudanar da zaben na nufin cewa Bashar Assad zai ci gaba da rike matsayinsa na shugabancin kasar.

To sai dai ko shakka babu zai kasance abu mai wuya a gudanar da wannan zabe a wasu yankuna na kasar sakamakon tashe-tashen hankulan da ake fama da su yanzu haka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.