Isa ga babban shafi
Syria

Ana shirin bude rijistar masu sha’awar takarar mukamin shugaban kasa a Syria

A kasar Syria, an saka ranar 21 ga watan Aprilu a matsayin ranar da za a fara rijistar sunayen wadanda ke da sha’awar tsayawa takarara shugaban kasar Syria.

Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad REUTERS/SANA/Handout via Reuters
Talla

Gwamnatin kasar ta Syria ta sha alwashin gudanar da zaben kamin wa’adin shugaba Bashar al-Assad ya kare a ranar 17 ga watan Yuli mai zuwa.

“A ranar litinin 21 ga watan Aprilu, kwamitin wakilai zai zauna domin bude rijistar masu sha’awar tsayawa takarar shugabancin kasa, kana su saka ranar da za a yi zaben.” Inji wata majiya a bangaren gwamnatin kasar.

Wannan zabe shi zai kasance zabe mai dauke da ‘yan takara da dama bayan da sabon kundin tsarin mulkin kasar ya kawar da tsarin jin ra’ayoyin mutane kamin a zabi shugaban kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.