Isa ga babban shafi
Malaysia

Malaysia: An sake hango wasu abubuwa kamar tarkacen jirgi a teku

Mahukuntan kasar Australia sun ce jiragen saman kasar da ke aikin neman jirgin kasar Malaysia da ya bata, sun sake hango wasu abubuwa a wani yanki na tekun India, bayan kwashe makwanni uku ana neman jirgin mai dauke da fasinja 239.

Hoton tauraron da ya hango wasu abubuwa masu kama da tarkacen jirgin Malaysia da ya bata
Hoton tauraron da ya hango wasu abubuwa masu kama da tarkacen jirgin Malaysia da ya bata ©REUTERS/Huang Shubo/Xinhua
Talla

Yanzu Jiragen ruwa da na sama ne ke ci gaba da aikin neman jirgin saman kasar Malaysia da ya bata, inda ake kyautata zaton, jirgin ya yi hatsari ne a cikin tekun India.

A jimilce jiragen sama 17 wadanda ke dauke da mutane da kayan aikin da kuma wasu manyan jiragen ruwa guda shida ne ke kan gudanar da wannan aiki ba dare ba rana akan tekun na India.

Masu binciken na aiki ne a filin da ya kai murabba’in kilomita dubu 319 a kan teku,

Kasar Amurka ce ta samar da jiragen sama bakwai, sai China da ta samar da biyu, akwai daya daga Koriya ta Kudu, yayin da kasashen New Zealand da Australiya da kuma Japan suka samar da sauran jiragen.

A can kuwa kan teku, yanzu haka akwai wasu jiragen ruwa guda shida dauke da ma’aikata da kuma na’uorin hangen nesa da ke gudanar da aikin tare da takwarorinsu da ke taimakawa daga sararin samaniya, kuma China da Australiya ne suka bayar da jiragen na ruwa.

Amma duk da haka, babu wata alama da ke iya gamsar da duniya cewa za a iya gano wannan jirgi da ya bata dauke da mutane 239 a cikinsa yau kusan makwanni uku ke nan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.