Malaysia: An dakatar da neman jirgi saboda matsalar yanayi
A karo na biyu cikin mako guda, an dakatar da neman jirgin kasar Malaysia na wuccin gadi wanda ya bata dauke da Fasinja 239 kusan makwanni uku, saboda matsalar kyawon yanayi a yankin tekun India, inda ake kyautata zaton jirgin ya fadi.
Wallafawa ranar:
A cewar hukumar da ke kula da ayyukan ruwan kasar Australia da ke jagorancin neman jirgin, ba a ganin yankin tekun na India da kyau saboda rashin kyawun yanayin.
Jiragen kasashe da dama ne suke aikin neman jirgin na Malaysia, kuma wasu hutunan da Faransa ta hango a tauraron dan adam an ga wasu abubuwa masu yawa da ke kama da tarkacen jirgi a cikin tekun India.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu