Isa ga babban shafi
Malaysia-Australia

An sake hango wasu abubuwa da ake zaton jirgin Malaysia ne

A ci gaba da neman jirgin saman fasinjan kasar Malaysia da ya bata, makwanni 3 kenan da suka gabata, a yau wani tauraron dan adam ya hango buraguzan wasu abubuwa 122 da ake zaton cewa na wannan jirgi ne a kan Tekun Indiya.

Tauraron dan adam na nuna hotuna kan teku.
Tauraron dan adam na nuna hotuna kan teku.
Talla

Sabbin hotunan wadanda tauraron dan adam na hukumar kula da tsaron sararin samaniya ta kasar Faransa ta ce ta gano, suna warwatse ne a wani wuri da ke kan teku mai fadin murabba’in kilomita 400 a cewar ministan sufuri na kasar Malaysia Hishamuddin Hussein.

Hishammuddin ya ce akwai alamun da ke tabbatar da cewa abubuwan da aka hagon sun yi kama da na jirgin saman fasinjan kasar da ya bata dauke da mutane 239 a cikinsa.

A can baya dai taurarin dan adam na kasashen Australiya, China da kuma Faransa, sun sha bayar da rahotanni da ke cewa an hango wasu abubuwa masu kama da tarkacen wannan jirgi, to amma daga bisani sai a gano cewa ba shi ba ne. To amma ministan sufurin na Malaysia ya ce suna da kwarin gwiwa dangane da wadannan sabbin bayanai.

Wasu daga cikin abubuwan da aka hango a wannan karo har da wadanda ke da tsawon akalla mita 23 suna yawo akan ruwa, to sai dai suna da tazarar kilomita dubu 555 daga gabar ruwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.