Isa ga babban shafi
Tekun India

Malaysia: Kwararru zasu tantance tarkacen jirgi a teku

Kwararru daga Amurka sun isa kasar Australia dauke da wasu na’urori domin tantance tarkacen jirgin saman kasar Malaysia a yayin da ake ci gaba da neman Jirgin da ake tunanin ya fadi ne a tekun India sama da mako biyu.

'Yan uwan fasinjan jirgin Malaysia da ke juyayin 'Yan uwansu da har yanzu babu labari akansu
'Yan uwan fasinjan jirgin Malaysia da ke juyayin 'Yan uwansu da har yanzu babu labari akansu REUTERS/Jason Lee
Talla

Bayan an dakatar da aikin neman jirgin saboda matsalar yanayi, yanzu jiragen sama ne da dama daga Autralia da Amurka da New Zealand da China da Japan da Koriya ta kudu suka kaddamar da aikin lalaben jirgin a tekun India.

Tuni Firaministan kasar Australia Tony Abbott a zauren Majalisa yace suna kyautata zaton jirgin ya fadi ne a kusa da yankin kasarsu tare da ware minti daya domin juyayin wadanda ke cikin jirgin da ba ko shakka sun mutu idan jirgin ya fadi.

Har yanzu rashin ganin komi daga cikin jirgin na kara harzuka dangi da ‘yan uwan fasinjoji da ke jirgin.

A jiya an samu sabani tsakanin Wasu daga cikin dangin wasu fasinjojin a kasar China, inda jirgin za shi, bayan ya taso daga Kuala-Lumpur na Malaysia, da Jami’an tsaro, lamarin da har ya kai suka dambace da jami’an tsaro.

Wannan nema yasa wasu gwanayen sihiri na gargajiya irin na China, ke ikirarin bazama domin ganin sun gano inda wannan jirgi ya sagale.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.