Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra'ila ta kai hare haren martani a Gaza

Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare hare a zirin Gaza a cikin daren Alhamis domin mayar da martani ga hare haren rokoki da mayakan jihadi suka kai a yankunan Isra’ila. Shugaba Mahmud Abbas ya bukaci Isra’ila ta dakatar da hare haren don samun zaman lafiya.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da Ministan tsaro Moshe Yaalon sun zauna a kusa da Rokoki kirar M302
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da Ministan tsaro Moshe Yaalon sun zauna a kusa da Rokoki kirar M302 REUTERS/Amir Cohen
Talla

Rahotanni sun ce Mayakan a zirin Gaza sun sake harba rokoki guda biyar a kudancin Isra’ila bayan hare haren da Isra’ila ta kai da ziragen sama.

A jiya Laraba, mayakan Jihadi a Gaza, sun harba rokoki guda 50 a yankin kudancin Isra’ila, lamarin da janyo kakkausan suka daga Firaminista Benjamin Netanyahu.

Hari na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da Firaministan Birtaniya David Cameron, ya sauka a kasar Isra’ila domin yin ziyarar kwanaki biyu.

harin shi ne mafi muni tun bayan wasu hare hare da aka kai a shekarar 2012 yayin da aka yi wata arangamar ta kwanaki takwas.

Harin wanda reshen mayakan suka dauki alhakin kai wa, sun ce ramukon gayya ne ga hare haren saman da Isra’ila ta kai a ranar Talata a Gaza, wanda ya halaka mutane biyu.

Wani jami’in Isra’ila yace an kai harin rokokin ne a jere da jare, a wasu anguwanni inda wasu daga cikin rokokin suka sauka akan wani dakin karatu da wani gidan shan mai.

Yanzu haka Rahotanni na cewa Isra’ila ta sha alwashin mamaye yankin na Gaza wanda ta fice daga cikinsa a shekarar 2005.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.