Isa ga babban shafi
Isra'ila-Jordan

Isra’ila ta yi nadama akan kisan Alkalin Jordan

Isra’ila ta bayyana nadamarta kan yadda jami’anta suka kashe wani alkali Dan kasar Jordan, abinda ya haifar da matsalar diflomasiya tsakanin kasashen biyu. Israila ta zargi alkalin Raed Zeiter da kokarin kwace bindigar jami’an tsaro, zargin da Jordan ta yi watsi da shi.

Masu zanga-zangar adawa da kisan Alkalin Jordan suna kona tutar kasar Isra'ila a birnin Amman
Masu zanga-zangar adawa da kisan Alkalin Jordan suna kona tutar kasar Isra'ila a birnin Amman REUTERS/Muhammad Hamed
Talla

Ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana nadama kan lamarin, amma ba tare da neman gafara ba.

Sojin kasar Isra’ila sun ce Raed Zeiter wanda asalinsa Bafalasdine ne ya kai masu hari tare da kokarin yin harbin bindiga, lamarin da ya sa suka kashe shi.

Wannan Kisan alkakin a ranar Litinin ya haifar sabuwar baraka tsakanin Isra’ila da Jordan wadanda suka amince da yarjejeniyar zaman lafiya tsawon shekaru 20 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.