Isa ga babban shafi
China

An yanke wa matar da ke sace jarirai hukunci a China

Wata Kotun kasar China ta yanke hukuncin kisa kan wata likita Mace, da aka samu da laifin sacewa da kuma sayar da jarirai a kasar. Tuni aka fara cece-kuce kan batun a cikin kasar, akan matar da ta dade tana satar jarirai.

Zhang Shuxia,  da ke sayar da Jarirai a kasar China
Zhang Shuxia, da ke sayar da Jarirai a kasar China REUTERS/China Daily
Talla

Kotun tace ta sami likita Zhang Shuxia, da laifin satar jarirai 7, bayan da ta yaudari iyayen yaran, su bata ‘ya ‘yan, bayan ta yi karyar ba su da lafiya ko sun mutu.

Sai a bara aka gano munakisar da Zhang ke ta aikatawa, lokacin da ta cewa iyayen wani jariri cewa mahaifiyar na da cutar Tunjere wato syphilis, da kuma ciwon hanta, da tace za ta iya karbar jaririn, don haka suka amince suka bata dan.

Kotun tace daga baya likitoci sun bayyana wa iyayen cewa ba su da cutukan, lokacin kuma Zhang ta riga ta sayar da dan tare da wasu jarirai mata guda biyu, kan kudi dalar Amurka kusan dubu 10.

A wasu lokuta iyayen kan yarda su rabu da ‘ya ‘yan da ke da nakasa a kasar Sin, saboda dokar hana haihuwa fiye da daya, da kuma tsangwama da ake nuna wa yaran da ba su da koshin lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.