Isa ga babban shafi
Falastine

Mahmud Abbas ya nemi a gudanar da bincike kan mutuwar Arafat

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya nemi da a gudanar da bincike na kasa da kasa game da mutuwar tsohon shugaban Falasdinu Yaseer Arafat.

Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas Reuters/Mohamad Torokman
Talla

Wannan shine karon farko da shugaban ya nemi a gudanar da bincike game da mutuwar Yaseer Arafat tun bayan wani rahoto da masu bincike a kasar Switzerland suka wallafa dake nuna cewa guba aka sawa Arafat ya mutu.

Tun bayan mutuwar Arafat a ranar 11 ga watan Nuwambar shekarar 2004 a wani asibiti dake birnin Paris, Falasdinawa ke ta babatun kashe shi aka yi inda suka samu tabbacin zarginsu bayan wannan rahoto.

Shugaba Abbas so yake a gudanar da binciken domin gane wake da alhakin kisan Arafat kamar yadda Faransata ta nemi a bi diddigin mutuwar Firaministan Lebanon Rafiq Hariri.

To sai dai Abbas ya ce wannan bincike da ya nema a gudanar, ko kadan ba zai shafi tattaunawar zaman lafiya da suke yi da Isra’ila ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.