Isa ga babban shafi
Falastine

Fatah da Hamas suna sukar juna akan Bikin tunawa da mutuwar Yaseer Arafat

Kungiyar Fatah ta Falasdinawa ta zargi kungiyar Hamas mai mulkin Gaza da hana ta gudanar da bikin juyayin mutuwar shugaban su Yaseer Arafat, wanda yau ya cika shekaru tara da mutuwa.

Wani Bafalasdine dauke da tuta mai hoton tshon jagoran Falasdinwa Yaseer Arafat
Wani Bafalasdine dauke da tuta mai hoton tshon jagoran Falasdinwa Yaseer Arafat REUTERS/Oleg Popov/Files
Talla

Kungiyar ta ce, shugabanin Hamas na cigaba da kama jami’an su dan ganin ba a gudanar da bikin na yau ba.

Arafat ya rasu ne ranar 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2004, inda wani bincike da aka gudanar kan gawar sa ya nuna sinadarin polonium ne ya kashe shi.

Yanzu haka Falasdinawa na neman a gudanar da bincike game bayan fitar wannan sakamako suna kuma kira ga kasar Faransa da bayyana nata sakamakon musabbin mutuwar Arafat.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.