Isa ga babban shafi
Syria

Jiragen yaki sun yi lugudan wuta a yankunan ‘Yan tawayen Syria

Rahotanni daga Syria na nuna cewa, Jiragen yaki na ta lugudan wuta a yankunan ‘Yan tawayen Syria, a yayin da aka nemi kasar Sin ta tallafa wajen kawo karshen tashin hankalin, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 180 a jiya. A cewar rahotanni, akalla hare –hare guda biyar a garin Damascus inda aka kashe fararen hula 30 cikinsu harda yara guda biyar.  

Hayaki ya turnuke wani yankin kasar Syria
Hayaki ya turnuke wani yankin kasar Syria REUTERS/STRINGER
Talla

Kungiyar nan mai saka ido akan rikicin na Syria ta ce wadanda akan kashe suna cikin mutane 182 da aka kashe a jiya Talata.

Sabon fada dai ya barke a yau Laraba, a yayin da ‘Yan tawayen suka kai hari kan dakarun da wajen binciken ababan hawa a Maaret al – Numan.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya da kasashen larabawa na musamman, Lakhdar Brahimi, ya yi kira ga kasar Sin da ta taimaka wajen ganin an kawo karshen wannan rikici.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.