Isa ga babban shafi
Syria

Bangarorin Syria sun amince su tsagaita Wuta Saboda Salla

Mai shiga tsakanin sasanta rikicin kasar Syria Lakhdar Brahimi yace Gwamnatin Syria da ‘Yan tawaye da ke Yaki da juna sun amince su tsagaita wuta albarkacin bukukuwan Salla da za’a fara a ranar Jumu’a bayan ya gana da Shugaban kungiyar Larabawa Nabil Al Arabi a birnin Al Kahira.

Wani Sojan 'Yan Tawayen Syria Azaz
Wani Sojan 'Yan Tawayen Syria Azaz Ruth Michaelson
Talla

Mista Brahimi yace sun tuntubi kwamandan ‘Yan tawaye Syria da dama kuma sun amince su tsagaita wuta a bukin Salla. Kuma yace a ranar Alhamis ne Gwamnatin Syria zata fito ta bayar da sanarwar tsagaita wuta a hukumance.

Sai dai kuma a yau Laraba jiragen yakin Syria sun kai hari a kauyen Idlib da ke arewa maso Yammcin kasar kuma harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 5 da suka hada da mata da kananan yara.

Tuni kuma Sarki Abdallah bin Abdulaziz na kasar Saudi Arabiya, ya bayyana dauwarsa kan halin da kasashen Musulmai ke ciki, da kuma rashin hadin kan kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.