Isa ga babban shafi
Syria

Lugudan wuta ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 20 a Syria

Akalla mutane 20 sun rasa rayukansu a wani lugudan wuta da dakarun gwamnati su ka yi akan wani yankin ‘Yan tawaye da ke Arewacin kasar Syria a yau. Kungiyar kare hakkin Bil Adaman kasar Birtaniya da ke saka ido akan rikicin na Syria ta bayyana hakan.  

Hayaki ya turnuke wani yankin garin Aleppo da ke Syria
Hayaki ya turnuke wani yankin garin Aleppo da ke Syria Reuters/路透社
Talla

Shugaban kungiyar, Rami Abdel Rahman ya bayyanawa Kamfanin Dillancin labaran AFP cewa harin wanda dakarun kasar su ka kai a garin Aazaz ya na kusa da garin Aleppo.

Wanann harin ya zo a dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke ikrarin cewa dakarun kasar ta Syria da kuma ‘Yan tawaye sun tafka laifukan tauye hakkin Bil Adama a rikicin na Syria wadanda su ka hada kisa, da azabtarwa da kuma yin fyade.

Sai dai kungiyar ta ce laifukan da ‘Yan tawayen su ka aikata basu kai na dakarun na gwamnati ba.

Wani rahoto mai shafi 102, wanda kuma za a gabatar da shi a gaban kwamitin kare hakkin Bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, ya nuna cewa yanayin kayayyakin soji da aka yi amfani da su a rikicin na Syria manya ne.

A nasu bangaren, rahotan ya nuna cewa su ma ‘Yan tawaye na da nasu laifuka sai dai yanayin na su da yawanshi bai kai yawan na dakarun gwamnati ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.