Isa ga babban shafi
Saudi-Syria

Shugabannin kasashen Musulmi za su gana a Makkah game da Syria

Shugabannin kasashen Musulmi a Yankin Gabas ta Tsakiya za su gudanar da taro a Makkah kasar Saudiya domin tattauna rikicin kasar Syria. Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad, yana cikin shugabannin da suka halarci taron duk da sabanin ra’ayi tsakanin shi da Sarki Abdallah wanda zai jagoranci Taron.

Gwamnan birnin Makkah Yarima   Khaled al-Faisal  a lokacin da yake tarbar Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad wanda ke sanye da harami a filin saukar jirgin a Jedda.
Gwamnan birnin Makkah Yarima Khaled al-Faisal a lokacin da yake tarbar Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad wanda ke sanye da harami a filin saukar jirgin a Jedda. REUTERS/Saudi Press
Talla

Sakataren kungiyar Musulmi ta OIC Ekmeleddin Ihsanoglu, yace rikicin Syria ne zai mamaye taron na shugabannin kasashen kungiyar 57. Ana sa ran kasashen za su kada kuri’ar dakatar da wakilcin Syria a Kungiyar.

Taron na kwanaki biyu na zuwa ne a dai dai lokacin da rikici ke ci gaba da kazanta a birnin Aleppo tsakanin dakarun gwamnatin Bashar Assad da ‘Yan Tawaye.

Masu sa ido a rikicin Syria sun ce sama da mutane 21,000 suka mutu tun fara zangar zangar adawa da gwamnatin Bashar al Assad watanni 17 da suka gabata.

Gwamnatin Iran ta dade tana zargin Saudi Arebiya da Qatar da Turkiya wajen tallafawa ‘Yan Tawaye da makamai.

A taron makon jiya da aka gudanar a kasar Iran game da rikicin Syria, wakilan kasar Saudiya sun kauracewa Taron wanda ya hada kasar Rasha da China maso goyon bayan gwamnatin Bashar al Assad.

A daya bangaren kuma ‘Yan adawa a Syria da gwamnatin Amurka sun zargi kasar Iran da taimakawa gwamnatin Assad da dakarun Soji amma Iran ta karyata zargin.

A Taron Saudiya dai ba a gayyaci ‘Yan adawa ba a Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.