Isa ga babban shafi
Iran-Syria

Kasashe 29 na duniya sun bukaci tattaunawa tsakanin al'ummar kasar Syria

An fara wani zaman taron tuntubar juna, da kasar Iran ta shirya na kasashe aminan gwamnatin kasar Syriya a birnin Tehran na kasar jamhuriyar musulunci ta Iran, a ganban wakilan kasashe 29 na duniya, wadanda suka soma zaman taron a jiya alhamis da yin kiran buda soma tattaunawa tsakanin al’ummar kasar Syriya.

Mahalarta taron tuntubar juna kan rikicin  kasar Syriya a Tehran na kasar Iran
Mahalarta taron tuntubar juna kan rikicin kasar Syriya a Tehran na kasar Iran IRNA
Talla

Ministan harakokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi da ya jagoranci zaman taron kasashen a gaban wakilan kasashen Chana Rasha, Pakistan da Iraki, ya bayyana cewa, dayawa daga yan adawar kasar ta Syriya sun bayyana amincewa shiga tattaunawa da gwmnatin kasar Syriya.

A daidai lokacin da kasashen aminan Syriya ke gudanar da taron nasu a jiya, Jakadiyar Amruka a majalisar dinkin duniya, uwargida Susan Rice, ta zargi kasar Iran da taka muguwar rawa a rikicin kasar ta Syriya

Rice ta kara da cewa, babu tantama Iran na taka muguwar rawa a rikicin na Syriya, kai ba ma Syriya kadai ba, a daukacin yanki gabas ta tsakkiya, ganin irin gagarumin goyon bayan da take baiwa gwamnatin Bashar al-Assad.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.