Isa ga babban shafi

Faransa da Jamus na karɓar baƙuncin taron nema wa Sudan tallafi a Paris

Faransa tare da haɗin gwiwar Jamus na karɓar baƙuncin taron ƙasa da ƙasa a birnin Paris, domin tara kuɗaɗen tallafin da za a yi amfani da su wajen taimaka wa miliyoyin mutanen da yaƙin Sudan ya tagayyara.

Birnin Khartoum yayin gabza ƙazamin faɗa tsaƙanin sojojin gwamnatin Sudan da dakarun RSF da suka yi tawaye. 1 ga Mayu, 2023.
Birnin Khartoum yayin gabza ƙazamin faɗa tsaƙanin sojojin gwamnatin Sudan da dakarun RSF da suka yi tawaye. 1 ga Mayu, 2023. REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

A yau Litinin 15 ga watan Afrilu yaƙin na Sudan da ya kazanta ke cika shekara cif da ɓarkewa, wanda kawo yanzu ya raba miliyoyin mutane da muhallansu baya ga rayukan wasu dubun dubatar da suka salwanta.

Taron neman taimakon na birnin Paris na zuwa a yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin agaji suka yi gargaɗi kan munin bala’in yunwar da ke addabar mutane fiye da miliyan 8 da yaƙin na Sudan ya shafa, sakamakon gaza isar da tallafin abinci da magunguna ga akasarin waɗanda suka tagayyaran.

Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da yakin Sudan ya raba da muhallansu.
Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da yakin Sudan ya raba da muhallansu. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA

A nata rahoton da ta fitar, kungiyar kare haƙƙin yara ta kasa da kasa ‘Save the Children’ ta ce  yanzu haka ƙananan yaran fiye da miliyan 10 yaƙin Sudan ya rutsa da su, wanɗanda suka gaza tserewa daga yankunan da ake gwabza ƙazamin faɗa a cikinsu da nisan fiye da kiomita 5.

Ya zuwa yanzu rikicin na Sudan ya raba mutane aƙalla miliyan 8 da muhallansu, adadin da ya kunshi mutane miliyan 6 da dubu 700 a cikin ƙasar, yayin da wasu miliyan 1 da dubu 800 suka tsere zuwa makwaftan ƙasashe.

Yanzu haka kimanin mutane miliyan 3 da dubu 400 ke buƙatar agajin gaggawa a Chadi kaɗai, sakamakon kwararar dubban ‘yan gudun hijira daga Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.