Isa ga babban shafi

Yaƙin Sudan ya cika shekara ɗaya da ɓarkewa

A yau Litinin yaƙin Sudan ke cika shekara guda cif da ɓarkewa tsakanin dakarun rundunar RSF da suka yi tawaye a karkashin jagorancin Muhammad Hamdan Daglo da kuma sojojin gwamnatin shugaba Abdul Fattah al-Burhan, bangarorin da dukkaninsu ake zargi da aikata laifukan yaki.

Yadda hayaki ya turnuƙe wani yankin Khartoum babban birnin kasar Sudan bayan kazantar yakin da ya ɓarke tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF da suka yi tawaye. 8 ga Yuni, 2023.
Yadda hayaki ya turnuƙe wani yankin Khartoum babban birnin kasar Sudan bayan kazantar yakin da ya ɓarke tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF da suka yi tawaye. 8 ga Yuni, 2023. AP
Talla

Rikicin da ya kazanta bayan ɓarkewarsa a ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2023, yayi sanadin mutuwar dubban mutanen da har yanzu ba a tattara adadinsu ba a hukumance.

Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya na baya bayan nan, ya ce yakin na Sudan ya tilasta wa dubban ‘yan kasar tserewa zuwa makwaftan kasashe musamman ma Chadi.

Wasu 'yan Sudan da rikici ya raba da muhallansu yayin kokarin ficewa daga birnin Khartoum. 19 ga Yuni, 2023.
Wasu 'yan Sudan da rikici ya raba da muhallansu yayin kokarin ficewa daga birnin Khartoum. 19 ga Yuni, 2023. AP

Rikicin ya kuma jefa miliyoyin mutane cikin bala’in yunwa, gami da haddasa yi wa dubban fararen hula kisan gilla saboda kabilanci, baya ga cin zarafin mata ta  hanyar fyade a yankin Darfur wanda dama yayi fama da kazamin rikici tsawon shekaru da dama.

A ranar Lahadi, Amurka ta ce za ta ware dala miliyan 100 don tallafa wa wadanda yakin na Sudan ya tagayyara.

Shugabar Hukumar Raya Kasashe Ta Amurka USAID Samantha Power, ta ce za a ayi amfani da miliyoyin dalar wajen samar da tallafin abinci, da magunguna, da kuma sauran kayayyakin bukatu ga wadanda rikicin ya ɗaiɗaita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.