An tono gawar Thomas Sankara
Yau litinin aka tono gawar tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara wanda aka kashe a shekarar 1987 lokacin wani juyin mulki da hambararren shugaban kasar Blaise Campoare ya aiwatar.Sai dai kuma masana na gani cewar an gudanar da haka ne domin kara kuntatawa Blaise Comporea.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ma’aikatar shari’a ta kasar ce ta tabbatar da haka, inda ta ce an tono gawar Sankara da wasu sojoji 12 da aka kashe lokacin juyin mulkin, inda kwararri daga kasar da kuma Faransa za su binciki yanayin da mutanen 13 suka rasa rayukansu.
Tun dai acikin watan maris daya gabata ne mahukunta kasar, suka umarci sake tona gawarwaki domin sake yi musu jana'iza acikin mutunci da girmamawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu